Sunday, 1 December 2019

Liverpool ta kara bada tazara a Teburin Premier League: Chelsea da Man City sun rasa maki

Liverpool ta yiwa Brighton ci 2-1 a wasan da suka buga jiya na gasar con kofin Premeir League na kasar Ingila inda da wannan nasara suka bayar da tazarar maki 11 a saman teburin Premier League.Dan wasan baya na Liverpool, Virgil Van Dijk ne ya ci mata duka kwallaye biyun da kai, shine dan kwallo na farko a kakar bana daya ci kwallaye 2 da kai a wasa daya a gasar ta Premier League saidai Brighton ta farko kwallo 1 inda a haka aka tashi wasa 2-1.
Saidai Liverpool ta kammala wasan da 'yan kwallo 10 bayan da aka baiwa Golanta, Alisson jan kati Ana mintuna 76 da wasa sanadin kama kwallo da yayi a wajan layin da aka yadda ya kama.

Man City da Newcastle sun buga 2-2 a wasa me zafi, Sterling da De Bruyne ne suka ciwa City kwallayenta. Kwallon De Bruyne ta dauki hankula sosai.
Chelsea ta yi rashin nasara a hannun West Ham da ci 1 me ban haushi.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment