Wednesday, 4 December 2019

Liverpool ta wa Everton cin tafi karfinka 5-2

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ci gaba da zama a matsayin ta daya a kan teburin Premier League bayan da ta wa Everton cin nafi karfinka na 5-2 a wasan da suka buga a daren yau.Origi ne ya fara cin kayatacciyar kwallon farko da Mane ya bashi sannan sai Shaqiri ya ci kwallo ta 2 da itama Mane ya bashi. Origi ya ci kwallo ta 3 me kayatarwa sosai sannan sai Mane yaci kwallo 4 wadda Alexander Arnold ya bashi itama me kayatarwa, Everton ta farko kwallaye 2 kuma a haka aka je hutun rabin lokaci 4-2.


Saidai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ana mintin karshe na tashi Wijnaldum ya ciwa Liverpool kwallo ta 5.
Alexander Arnold na ya bada taimako anci kwallaye 18 daga kakar wasan bara zuwa yanzu inda a shekararnan kawai ya bayar da taimako aka ci kwallaye 15, babu dan wasan da ke da wannan tarihin a Premier League a yanzu.

Kalli kwallon da Dejan Lovren ya baiwa Origi ya ci a kasa data dauki hankula:

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment