Wednesday, 4 December 2019

Man City ta lallasa Burnley da ci 4-1: Mahrez ya kafa Tarihi

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta wa Burnley ci 4-1 a wasan da suka buga jiya na gasar cin kofin Premier League na kasar Ingila. Gabriel Jesus ne ya fara ciwa City kwallaye 2 sannan Rodri ya ci mata ta 3.Riyad Mahrez dan kasar Algeria ne ya ciwa City kwallon ta ta 4 wqdda kuma itace kwallo ta 50 da yaci a gasar inda ya shiga jerin 'yan Afrika 9 da suka taba cin kwallaye 50 a gasar sannan dan kasar Algeria na farko da ya taba cin kwallaye da yawa haka:

A baya Emmanuel Adebayo, Nwakwo Kanu, Yakubu Aiyegbeni, Mohamed Salah, Sadio Mane, Yaya Toure, Didier Drogba, Efan Ekoku duk suna da kwallaye 50 a gasar ta Premier League in Ingila.

Da wannan nasara, Man City ta koma matsayi na 2 a teburin gasar:

Kalli maimaicin kayatattun kwallayen da aka ci jiya a wasan:


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment