Wednesday, 4 December 2019

Me kamfanin Facebook zai bayar da kashi 99 cikin 100 na dukiyarshi dan tallafawa Mutane

Me kamfanin Facebook wanda kuma shine mutum na 5 da ya fi kowa kudi a Duniya, Mark Zuckerberg da matarshi Priscilla Chan sun sha alwashin bayar da kaso 99 na kudin da suka mallaka wqjan tallafawa mutane.
Ma'auratan sun dauki wannan alkawarine a wata hira da suka yi da gidan talabijin na CBS dake kasar Amurka inda suka bayyana cewa, zasu bayar da dukiyar tasu ne ga gidauniyarsu dake tallafawa samar da Ilimi ga kowa da kuma samar da magunguna ga ciwukan da musamman basa jin magani.

Sun bayyana cewa burinsu shine samar da maganin kowace irin cuta da ake fama da ita a wannan karni.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment