Monday, 2 December 2019

Messi da iyalanshi sun isa Faransa halartar taron bayar da kyautar Ballon d'Or: Ronaldo ba zai halarta ba

Tauraron dan kwallon kasar Argentina me bugawa kungiyar Barcelona wasa, Lionel Messi kenan a wadannan hotunan tare da iyalanshi a yayin da suka isa kasar Faransa wajan da za'a bayar da kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Duniya da kowane dan kwallon kafa ke burin lashewa watau Ballon d'Or.Messi da abokin takararshi Ronaldo nada kyautar guda 5-5. Saidai a wannan karin wani labarin sirri ya bayyana kan wanda zai lashe kyautar kuma an bayyana cewa Messi ne.

Idan hakan ta tabbata dai Messi zai zama yana da kyautar guda 6 kenan wanda shi kadai ke da irin wannan tarihi.

Ta bangaren Ronaldo kuwa rahotanni sun tabbatar da cewa bazai halarci wajan bayar da kyautar ba saboda akwai wani taron na daban da zai halarta wanda za'a karramshi da wasu kyautuka.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment