Sunday, 1 December 2019

Messi ya ciwa Barca kwallo 1 data bata nasara akan Atletico Madrid

A yayin da wasa yayi zafi tsakanin Barcelona da Atletico Madrid, Golan Barca Ter Stegen ya taimakawa kungiyar sosai a zagayen farko kamin a je hutun rabin lokaci inda ya tare kwallaye kusan 2 masu kyau wanda da yayi sakwa-sakwa dasu da sun shiga raga.
Saidai bayan dawowa daga hutun rabin Lokacine,Messi ya lika musu kwallo 1 me ban haushi kuma a haka aka tashi wasan 1-0.
A lokacin da yake murnar cin kwallonshi, Messi ya rika kakkabe bajen Barcelona wanda hakan ke nuna yanda yake Alfahari da kungiyar.
Wannan ne karin farko da Griezmann ya koma Atletico Madrid tun bayan barinshi kungiyar zuwa Barca.

A yau Barcelona ta saka sabuwar rigar kwallo da ta yi wasa da ita.

Da wannan nasara Barca ta sake darewa saman teburin gasar La liga.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment