Monday, 2 December 2019

Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 6: Drogba ya dauki hankula sosai a wajan taron

Tauraron dan kwallon kafar kasar Argentina me bugawa Kungiyar Barcelona wasa, Lionel Messi ya kafa tarihi a yau inda ya shiga gaban babban abokin takararshi a harkar kwallon kafa, Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Ballon d'Or ta bana.
Yanzu Messi na da kyautar guda 6 kenan yayin da Ronaldo ke da guna 5.

Messi ne kadai ya taba kafa irin wannan tarihi a Duniya.

A lokacin bayar da kyautar, tsohon tauraron dan kwallon Chelsea Didier Drogba ya dauki hankula inda da farko ya dauki hoton dauki da kanka me cike da tarihi da matashin dan kwallon PSG, Kylian Mbappe, Dalilin daukar hoton kuwa shine, shekaru 10 da suka gabata bayan wasan da Chelsea ta buga da Barcelona na gasar cin kofin Champions League, wani yaro ya tunkari Drogba inda yaso daukar hoto dashi amma Drogban ya ki amincewa da daukar hoton saboda bacin ran hukuncin Rafali, Drogba yace daga baya ya gane cewa yaronnan ashe Kylian Mbappe ne.

Dan haka a lokacin daukar hoton ya bukaci duk mutanen dake dakin taron suka tashi tsaye aka dauki hoton.

Dalili na biyu da ya sa Drogba ya dauki hankula musamman ga 'yan Najeriya shine da aka ganshi rike da wayar iphone 6 yayin da matasa, mata da maza ke yayin iphone 11. Wannan dalili yasa da yawa sukace hamshakin mekudi irin Drogba yayi amfani da iphone 6 ai kuwa suma basu ga dalilin da zaisa suce sai run rike wayar kece raini ba.Virgil Van Dijk ne yazo na 2

Sai Ronaldo ya zo na 3

Sai kuma Sadio Mane ya zo na 4Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment