Sunday, 1 December 2019

Mourinho ya ci wasa na 3 a jere a matsayin kocin Tottenham: Abubuwan kayatarwar da suka faru a wasasu na jiya

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta lallasa Bournemouth da ci 3-2 a wasan da suka buga jiya na gasar cin kofin Premier League na kasar Ingila. Lamba 10 na kungiyar wamda tun kama aikin Mourinho a matsayin kocin kungiyar, Dele Alli ne ya ci kwallaye 2 shi kadai.Moussa Sissoko ya ci kwallo ta 3 me kayatarwa  wadda kuma itave kwallonshi ta farko a cikin shekaru 3. Duk da cewa Bournemouth ta farke kwallaye 2 amma an tashi wasan 3-2.Wannan ce nasara ta 3 a jere da Tottenham ta samu tun fara aikin Mourinho sannan nasara ta 2 a gasar Premier League sannan kuma nasarasu ta farko a wasansu a gida.

Wannan nasara ta baiwa Tottenham damar kaiwa matsayi na 5 akan teburin Premier League, saidai sai an buga wasannin yaune za'a san ko zata tsaya a wannan matsayi ko kuwa zata rikoto.

A wasan na jiya ma an samu yaronnan da ya bayar da kwallo da sauri a wasan Tottenham da Olympiacos wadda ta yi sadain shiga raga ya kara daukar hankula inda bayan cin kwallon Dele Alli ta farko Mourinho ya tashi yaje suka sha hannu da yaron.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Mourinho ya gayyaci yaron inda suka ci abinci tare da 'yan wasan kungiyar kuma yasha alwashi ci gaba da yin hakan tare da sauran yaran kwallon kungiyar.

Crystal Palace ta lallasa Burnley da 2-0.

Sai Southampton ta wa Watford 2-1

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment