Wednesday, 4 December 2019

Mourinho yayi rashin nasara a karin farko a hannun Man United: Karanta sauran kayatattun labaran yanda ta kasance a wasannin na yau

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta lallasa Tottenham da ci 2-1 a wasan da suka buga a daren yau na gasar cin kofin Premier League inda Rashford ya ci wa Man U duka kwallayen guda 2 sannan Dele Alli shi kuma ya ciwa Tottenham kwallon ta.Wannan ne karin farko da Mourinho ya koma filiin wasan Man United a matsayin koci bayan da suka koreshi kuma wannan ne wasa na farko da yayi rashin nasara tun bayan kama aiki a matsayin me horas da 'yan wasan Tottenham din inda a baya yaci wasanni 3 a jere.


Dama dai Man United na da tarihin cin Tottenham inda ta ci ta sau 38. Da kwallayen da yqci yau, Rashford na da kwallaye 6 kenan a kakar wasan bana bayan buga wasanni 10.

Ana cikin wasan 'yan kwallo sun fada kan Mourinho bisa kuskure inda suka buge mai kafa kuma abin ya dauki hankula.


Kwallon da Dele Alli yaci ta dauki hankula kuma da alama dai yana ta kara muurewa a karkashin horaswar Mourinho inda a yanzu yake da kwallaye 4 a wadanni 4 daya buga da Mourinhon.


Leicester City ta sake darewa Matsayinta na 2 akan saman teburin Premier League bayan da Man City ta danashi a jiya bayan tawa Watford ci 2-0. Jamie Vardy ne ya ciwa Leicester kwallon ta ta farko wadda kuma itace kwallo ta 50 da ya ciwa kungiyar sannan Maddison yaci kwallo ta 2.

Chelsea ta ci gaba da zama a matsayi na 4 akan teburi  Premier League bayan da ta wa Aston Villa ci 2-1. Tammy Abraham ne ya ci mata kwallon farko wadda kuma itace kwallonshi ta 11 a wasanni 14 da ya buga a bana sai kuma Mason Mount da ya ci kwallo ta ta 2.

Itama Wolves ta wa West Ham 2-0.

Sai Saothampton da tawa Norwich 2-1Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment