Monday, 2 December 2019

Mutane na caccakata ne saboda abinda mahaifina yayi>>Zahara Buhari

Diyar shugaban kasa,Zahara Buhari ta bayyana cewa da yawan wadanda suke caccakarta da kaya mata kalaman da basu dace ba a shafukan sada zumunta suna yi ne saboda wasu abubuwa da mahaifinta, shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi.

Ta bayyana cewa amma takan yiwa irin mutanennan addu'ane kuma ta ci gaba da ratuwarta.

Zahara ta bayyana hakane a wajan taron tattaunawar da ta yi da mutane kan yanda take samun takala da kalaman kiyayya a shafukan sada zumunta, taron da gidauniyarta ta tallafawa gajiyayyu ta shirya da aka biya Naira Dubu 10,000 dan shiga wanda kuma ya jawo cece-kuce sosai.

Taron ya jawo Matasa kuma Zahara ta bayyana cewa, ta fara samun itin kalaman caccaka a shafinta na sada zumuntane tun daga shekarar 2015. Tace akwai wani hoto da take Atisayen Yoga da aka rika watsa shi inda wasu suka rika amfani dashi dan samun ribar kansu, tace amma abin sai ya juya ya zama alheri dan da yawa sunsha basu yi karatu ba sun sha cewa kowa a Arewa jahiline.

Tace amma dalilin haka sun gane cewa suna da ilimi kuma sun iya turanci.

Tace bayan an kammala zabe sai kuma daga baya ta rika samun sakonnin cewa, Zahara babanki yayi kaza-da-kaza.

Tace shin abinda take tambaya ita tana cikin gwamnati ana gudanar da harkar gwamnati tare da ita?

Tace abinda masu kalaman takala da kiyya ke yi suna yi ne saboda suna kishin nasarar da mutum ke da ita, suna ganin cewa dama ace sune, tace kuma suna so su sa ka rasa wannan nasara da ka samu, tace to zaka biye musu? Zahara ta bayar da shawara ga wadanda ke fama da irin wannan abu da kada su biyewa masu takalar tasu, maimakon haka su musu addu'a.

Zahara ta kuma bayyana ra'ayinta kan dokar kalaman kiyayya da majalisar tarayya ke shirin sakawa cikin doka inda tace tana goyon bayan dokar amma wadda aka yi bisa tsarin da ya kamata.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment