Tuesday, 3 December 2019

Naira Dubu 7 mahaifina ya mutu ya bari>>Dan Marigayi tsohon shugaban kasa, Janar Murtala Muhammad

Dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Murtala Ramat Muhammad, Risqua Murtala ya bayyana cewa mahaifinshi duk da yake shugaban kasa Naira dubu 7 kacal ya rasu ya bari a asusun ajiyarshi na banki.Risqua yayi wannan maganane a wajan kaddamar da mutum-mutumin mahaifinshi da aka yi a jami'ar Obafemi Awolowo a jihar Osun.

Ya bayyana cewa mahaifinshi yayi yaki da rashawa da cin hanci lokacin yana shugaban kasa inda ya yabawa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari da shima yake yaki da rashawa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment