Wednesday, 4 December 2019

Najeriya ce kan gaba na yawan malariya a fadin duniya

Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi gargadi kan yadda cutar zazzabin cizon sauro ke ci gaba da kwarzabar mata masu juna biyu da kananan yara a Afirka.


An fitar da rahoton ne don ranar tunawa da yaki da zazzabin cizon sauro mai taken World Malaria Day 2019.

Rahoton ya koka kan yadda aka karkace daga kokarin dakile mace-macen da cutar zazzabin cizon sauro ke haddasawa da rabi a duniya nan da shekara ta 2023.Akwai kuma burin Muradan Ci Gaba Mai 'Dorewa da ke rajin ganin an kakkabe cutar maleriya nan da 2030, shi ma ya karkace daga alkibla.

Rahoton dai ya fara da labari ne mai dadi na cewa an samu raguwar kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro cikin shekara ta 2018.

An bayar da rahoton kamuwa da zazzabin kan kasa da mutum 10,000 a cikin kasashe guda 49 da suke fama da maleriya, maimakon kasashe 40 a shekara ta 2010.

Haka kuma kasashe 27 sun ba da rahoton cewa kasa da mutum 100 sun kamu da cutar a bara, abin da d'ara kasa 17 a shekara ta 2010.

Wannan wani babban ma'auni in ji rahoton na cewa nesa ta zo kusa ga kokarin kakkabe maleriya.

An kuma bai wa kasa biyu Paraguay da Uzbekistan shaidar Hukumar Lafiya ta Duniya da ke tabbatar da cewa sun rabu da ja'ibar maleriya a 2018, a bana kuma karin kasashen Aljeriya da Argentina su sun yi nasarar kakkabe zazzabin.

Ana bayar da wannan shaida ce idan wata ta kafa hujjar yanka shakku na gwargwadon hankali cewa ta katse yaduwar zazzabin maleriyan da tun asali ake samu a can akalla tsawon shekara uku a jere.

Kasashe guda 38 ya zuwa yanzu suka kafa wannan tarihi.


Sai dai duk da wannan nasara, rahoton ya ce a shekarun baya-bayan nan ci gaban da aka samu a duniya wajen rage sabbin masu kamuwa da zazzabin cizon sauro na tafiyar hawainiya.

A bara, kiyasin mutum miliyan 228 ne ya kamu da maleriya idan aka kwatanta da miliyan 231 a bara waccan.

Haka kuma kananan yara 'yan kasa da shekara 5 ne suka fi yawan mutuwa da kashi 67 cikin 100 wato kashi biyu cikin uku na mace-macen da aka samu a duniya sanadin maleriya a 2018.

Haka zalika a nahiyar Afirka ne aka samu yawan mutanen da suka kamu da zazzabin da kashi 93 cikin 100 a shekara ta 2018 kuma fiye da rabi na wannan adadi ya faru ne a kasashe guda shida.

Nijeriya ce kan gaba da kashi 25 cikin 100 na yawan maleriya, sai Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo kashi 12, Uganda na da kashi 5 cikin 100 Kwatdebuwa da Mozambique da Nijar na da yawan masu maleriya kashi hudu kowaccensu.

Rahoton ya kuma ce a 2018, an samu kiyasin mutum miliyan 155 na adadin wadanda suka kamu da maleriya a kasashe guda 11 da ke cikin wani shiri mai taken High Burden High Impact da ke kokarin farfado da yaki da cutar maleriya bayan sun sauka daga layin kakkabe cutar.

Daga cikinsu kasa biyu Indiya da Uganda sun samu gagarumar nasarar rage yawan masu kamuwa da zazzabin a bara, idan an kwatanta da bara waccan.

Sai dai a Najeriya da Ghana gagarumar karuwar wadanda suka kamu da maleriya aka samu a 2018 idan an kwatanta da 2017, inda Najeriya ta sami karuwar mutum miliyan 3.4, ita kuma Ghana ta sami karuwar mutum rabin miliyan daya.
BBCHausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment