Thursday, 5 December 2019

Ni Ba'a burgeni>>Aina'u Ade, Laila

A hirar da ta yi da BBC a shirin daga bakin mai ita, Jarumar fina-Finan Hausa Aina'u Ade wadda aka fi sani da Laila ta amsa wasu tambayoyi ciki hadda waye saurayinta a Kannwood inda tace ita kadai take tafiyarta bata da Saurayi a masana'antar.
Da aka tambayi Aina'u ko wanene Gwarzon jaruminta? Ta bayyana cewa ita fa ba'a burgeta dan kuwa abinda bai dame ta ba ta kulashi.

Da aka tambayeta me ye bata so sai tace Karya,tace ta tsani karya dan ita da wuya ta yi karya shiyasa idan aka mata itama bata so.

Da aka tambayeta maganar soyayya tace to da da tana yarinya ta yi,lokacin mutum bai mallaki hankalin kanshi ba, tace kuma ita idan tana son mutum tana yi ne da zuciya 1 amma mutum na yi mata karya shikenan zata rabu dashi.

Da aka tambayeta wane irin tsegumi take so sai tace su mata tsegumi kamar hanjine in basu yi ba ma wani lokacin basa jin dadi dan wani lokacin ko da Ido ana yi.

Da aka tambayeta wace irin tambayace bata so? Aina'u ta bayyana cewa, tambayar kwa-kwa wanda mutum ya san abu ko kuma yana ganinshi amma yayi ta maka tambaya akai, Ta bayar da misalin cewa wata rana zata shiga banki sai ga wata ta tare ta suka gaisa faran-faran, sai take tambayarta ina motarki, Aina'u tace na bata amsar na sayar ko akwai wanda zai kamani?

Da aka tambayeta harkar waya da Chatin ta bayyana cewa,ita bata yi fa, sai ai ta mata magana ba bata mayarwa, ta kara da cewa wani sa'in ma ko wayar bata dame ta ba.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment