Tuesday, 3 December 2019

Nima Ban ji dadi ba a lokacin da Ronaldo ya ci Ballon d'Or na 5>>Messi

Bayan lashe kyautar Ballon d'Or na 6 tauraron dan kwallon kafar kasar Argentina me bugawa Barcelona wasa, Lionel Messi da yake magana akan rashin zuwan Ronaldo wajan bayar da kyautar yace ya fahimcin Ronaldon dan shima maganar Gaskiya a lokacin da Ronaldo ya ci na 5 be ji dadi ba.Messi ya bayyana cewa kamin Ronaldo ya ci Ballon d'Or na 5 shi kadaine me guda 5 amma kuma sai gashi Ronaldon ya kamoshi yace be ji dadi ba gaskiya a lokacin da aka baiwa Ronaldon kyautar amma ya fahimci cewa rashin cin Champions League da basu yi bane yasa be ci kyautar ba.

Messi ya kara da cewa ba abune me sauki ba mutum ya kwashe shekaru 10 yana fafatawa wajan cin gasar ba, yace sai me sa'a kuma shi ma yaji dadi yana da sa'a.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment