Tuesday, 3 December 2019

Ranar Masu Nakasa Ta Duniya: 'Ba zan taba daina bara ba'

Tun a shekarar 1992 Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Disamba domin ta zama Ranar Masu Nakasa Ta Duniya.


Sau da dama a Najeriya masu fama da larurar nakasa kan fada cikin halin bara a wani lokaci kuma wasu na kokarin yin sana'a domin neman na kansu.A wannan dalili ne ya sa BBC ta tattauna da wasu nakasassu a garin Abuja domin jin ta bakinsu kan dalilinsu na bara, da kuma kuma irin kalubalen da suke fuskanta a matsayinsu na nakasassu.

Wani daga cikin masu larurar nakasa da BBC ta tattauna da shi mai suna Abubakar Mohammed ya shaida mana cewa a dalilin rashin samun sana'a ne ya sa yake bara.


Shi kuma Ibrahim Abubakar ya ce rashin samun tallafi a matsayinsa na nakasashe ya sa ya shiga bara.

Ya ce sau da dama a kauyuka idan an bayar da tallafi ba ya zuwa garesu.

Ya ce a haka ba za a hana su bara ba, a cewarsa, sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi a kan bara idan ba za a tallafa musu ba.

Ko a shekarar bara sai da nakasassun suka gudanar da wata zanga-zanga a majalisar dokokin Najeriyar, bisa rashin ba su kulawa ta musamman wajen daukar aiki.

Sun ce suna da masu ilimi da dama a cikinsu da za su iya yin duk wani aikin gwamnati.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment