Sunday, 1 December 2019

Real Madrid ta hau na 1 a Teburin La liga: Ramos yaci mata kwallo sannan ya jawo an ci ta

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yiwa Deportivo Alaves ci 2-1 a wasan da suka buga jiya na gasar cin kofin La liga na kasar sifaniya. Dan wasan baya, Sergio Ramos ne ya fara ciwa Madrid kwallo inda Carvajal ya ci ta 2.Saidai bayan kwallon da ya ci, Ramos ya jawo Bugun daga kai sai Gola wanda sanadin haka Alaves ta farke kwallo daya, a haka aka tashi wasan 2-1 wanda ya baiwa Madrid damar hayewa saman teburin La liga da maki 31, wasa tsakanin Barcelona da Atletico Madrid na yaune zai tantance ko Madrid zata ci gaba da zama a matsayi na 1.

Da kwallon da ya ci, Ramos yana da jimullar kwallaye 3 kenan a bana duka da yana dan baya, hakan na nufin yafi Hazard da Gareth Bale cin kwallaye inda Hazard ke da 1 Bale na da 3.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment