Friday, 6 December 2019

Ronaldon Asali yana Brazil>>Ibrahimovic ya gayawa Cristiano Ronaldo

Tauraron dan kwallon Galaxy, Ibrahimovic ya fadawa Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo maganar da ba zai so jinta ba inda yace Ronaldon Asali yana Brazil.
Movic wanda a karshen watannan zai bar Galaxy kuma ana sa ran cewa Serie A zai koma amma bai bayyana ko wace kungiya ba an tambayeshi cewa watau zaka je ka hadu da Ronaldo na Asali kenan.

Saidai yace Ronaldon Asali ai dan kasar Brazil ne, Watau Ronaldo Nazario, inda yace shi Cristiano Ronaldo ai iya kwallonshi ba baiwa bace, dagiyace tasa ya iya kwallo.

Da yake magana akan cewa Ronaldo yayi kokari da ya koma Juventus, yace ba wani kokarin da yayi, dan kuwa tun kamin zuwanshi kungiyar ta daga kofin Serie A sau 7 dan haka da yana so ace yayi kokari sai yaje lokacin bana ta buga gasar Serie A ya kawo ta fara bugashi sannan a san shi gwanine.

Koda a shekarar 2018 da Luca Modric ya lashe kyautar kwarzon kwallon kafa ta Ballon d'Or, Movic ya yi martanin cewa ashe dama can me kungiyar Real Madrid,Florentino Perez ne ke lashe kyautar ba Ronaldo ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment