Wednesday, 4 December 2019

Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan Ziyarar aiki ta kwanaki 5

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya koma Fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta kwanaki 5 zuwa Malabo, Katsina da Kaduna.
Shugaban ya halarci taron kungiyar kasashen dake fitar da Iskar Gas a kasar Equatorial Guinea sannan ya zarce Katsina inda ya kaddamar da fara ginin jami'ar sufuri ta gwamnatin tarayya a Sandamu karkashin masarautar Daura da kuma wani aikin titi da jihar ta yi.

Hakanam shugaban ya halarci wajan taron shugaban sojoji na kasa a Kaduna inda ya kaddamar da sabbin motocin yaki kirar Najeriya da Asibitin Sojoji.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment