Sunday, 1 December 2019

Sojojin Najeriya da hadin gwiwar na makwabtan kasashe sun kashe Mayakan Boko Haram 13

Hadin gwiwar dakarun Najeriya da na kasashen yankin tafkin Chadi sun sake samun wani gagarumar nasara a wata fafatawa da suka yi a Arewacin jihar Borno.

Dakarun sashi na 3 na rundunar yaki da Boko Haram ta "Operation Lafiya Dole" da kuma sashi na 2 na dakarun hadin gwiwa na kasashen yankin tafkin Tchadi, sun sami nasarar ragargazar mayakan Boko Haram a tsibirin Duguri dake arewacin jihar Borno.

Jami'in sadarwa na aikace aikacen rundunar sojojin Najeryia, Kanar Aminu Ilyasu cikin sanarwar da ya fitar ya nuna cewa fafatawar ta auku ne a yunkurin dakarun na cimma kauyukan Njirwa da Duguru.

Bayan da dakarun suka cimma kauyukan biyu, kazakika sun kuma yi dirar mikiya akan yan bindigar Boko Haram din wadanda ke fada da wasu motoci hudu masu dauke da manyan bindigogin kai farmaki.

A dai fafatawar sojojin wadanda jiragen yaki suka tallafa masu, take sun hallaka kimanin mayakan Boko Haram goma sha uku tare da kwato motoci 4 masu dauke da manyan bindigogin kai farmaki da Karin wasu manyan bindigogin harbo jiragen sama dama wasu bindigogin kirar AK 47 da harsasai na musamman sama da Dari biyu.

A cewar wani masanin tsaro Manjo Bashir Shayibu Galma wannan nasara da dakarun suka samu tana nuna cewa lalle ana dab da kawar da burbushin yan ta'adda.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment