Tuesday, 3 December 2019

Ta kashe Diyar Kishiyarta ta Hanyar Sanya mata Guba a Abinci

Rundunar 'yan Sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina, Sanusi Buba ta yi nasarar damke Aisha Abubakar, 'yar shekara talatin da takwas da haihuwa dake Sabuwar Unguwa a karamar hukumar Rimi a jihar Katsina, bisa zargin kashe diyar Kishiyarta yar shekara hudu da haihuwa ta hanyar yin amfani da shinkafa bera.


Bayan cin abinci ne, aka garzaya da ita asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwar ta sakamakon cin abinci mai guba da ta ci.

Da manema labarai ke tambayarta dalilin da ya sa ta aikata wannan kisan kai, ta bayyana cewa sakamakon rashin jituwar da ke tsakanina da mahaifiyarta, da kuma kishi ya sanya na aikata wannan aika-aika, wadda nake da na sani a halin yanzu.

Ana cigaba da bincike, kuma wadda ake zargi ta amsa laifin da ake zarginta na kashe diyar kishiyarta.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment