Tuesday, 3 December 2019

Wannan hoton bidiyon da ya nuna yanda wasu yara suka yi bayan da Aka gaya musu cewa mahaifinsu ya rasu zai saka zubar da hawaye

Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan hoton ya tayar da hankalin kusan duk wanda ya ganshi, wasu yarane 'yan gida daya su biyu mace da namiji a kasar Syria suka fashe da kuka bayan da aka gaya musu cewa mahaifinsu, kakarsu sun rasu a wani hari da aka kaiwa wata kasuwa a kasar.Rahotanni sun bayyana cewa, Jirgin yakin Kasar Rasha ne ya kai harin a cikin kasuwa.

Yaran su biyu da ake iya ganinsu cikin jini suma sun samu sun tsirane daga harin sai aka zo aka gaya musu cewa mahaifinsu ya rasu.

Yarinyar da itace ta dan fi wayau ta tashi tana kuka tana cewa ku ce min babana bai mutu ba, Babana kada ka mutu.

Abin akwai ban tausai sosai.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment