Sunday, 1 December 2019

YABON GWANI YA ZAMA DOLE: AMFANIN DA MALAM AMINU DAURAWA KEWA AL-UMMA

Babu shakka samun Mutane irinsu Malam Shiekh Muhammad Aminu Daurawa a cikin wannan al'umma babban alkairi ne gami da rahama da jin kai daga wajen Allah, da yawan mutane basu san irin alkhairin da wannan bawan Allah ke aiwatarwa ba, wanda zan iya cewa bansan wani malami a ƙasar nan da zaiyi kunnen doki da Malam daurawa  wajen amfanar da al'umma ba.


Fiye da shekaru masu yawa Malam ya buɗe gidauniya a jahar gombe wacce ke ɗaukar nauyin rayuwar marayu da marasa galihu, tun daga yarintarsu har girmansu, abinda ya shafi karatunsu da ɗawainiyarsu, wannan gidauniya bata barinsu har sai ta koyar dasu wata sana'a ko an sama musu aikin da zasu rike kansu, tabbas wannan ba karamin alkhairi bane.

Har ila yau dai, wannan gidauniya kan ɗauki nauyin kula da rayuwar wanda ya shigo addinin musulunci, kowa shaida ne yadda Malam ke musuluntar da mutane a wajen tafsirinshi inda yake umartar kwamitin gidauniyarshi da ɗaukan nauyin wanda ya musulunta tun daga karatun addini har ya zuwa boko da sauran bukatunshi, da kuma sana'ar da zata dace da mutum a koya mishi, wannan kan ƙara karfin imani da Soyayyar musulunci a zukatan waɗanda suka musulunta.

Ina ma za'a samu irinsu Malam daurawa guda biyar a wannan ƙasa da an samu cigaba da alkhairi mai yawa, domin irinsu Malam daurawa ba abinda ke gabansu sai cigaban addini da ƙokarin karantar da mutane addini da musuluntar da maguzawa, saɓanin wasu malamai masu raba kawunan mutane, ban taɓa ji ba cikin karatun Malam Daurawa inda ya kama sunan wata qungiya ya aibata, hatta ƴan ɗariqa suna son malam suna sauraron karatunsa saboda adalci irin nasa, saɓanin malaman dake fakewa da sukar qungiyar da suke da saɓanin ra'ayi su ɗaukaka kansu, wanda malam ba haka yake ba, ilminshi da fasaharshi ne suka ɗaukaka shi.

Banji daɗin barin Malam Daurawa gidan hizba ba, domin ba ƙaramin taimakon addini da al'umma yake da wannan damar ba, musamman umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da kuma sulhunta mutane da ma'aurata, wanda su Umar Muhammad Assalafi ke ta ƙokari a lokacin, ni kaina shaida ne, nayi mu'amala da Malam akan wani muhimmin al'amari nan na fahimci malam mutum ne mai tawadi'u, saukin kai da girmama mutane, hakika malam daurawa ya cika siffofi da halayen ƴan Aljannah. 

Babu tantama Siyasa ce silar fitar Malam daga hizba, muna addu'a Allah yasa hakan ya zama alkhairi gareshi ya kuma kawo masa damar da tafi wannan wanda al'umma zasu amfana da ita.

In dai anaso al'ummarmu ta  cigaba dole malamanmu suyi koyi da  Malam daurawa baban Huzaifah Aminu Daurawa 

Muna addu'a Allah ya karawa Malam lafiya da imani, ya kara taimakonsa cikin ayyukansa, ya karawa rayuwarsa albarka yasa ya gama da duniya lafiya.

Aliyu Imam IndabawaKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment