Friday, 13 December 2019

Yanda dan Shekara 19 yawa Mahaifiyarshi ciki

Wani lamari me rikitarwa daya faru a jihar Delta ya dagawa jama'ar jihar Hankali inda aka samu matashi me shekaru 19 ya dirkawa mahaifiyarshi ciki a garin gwada lakanin soyayya da wani boka ya bashi.Bayan bayyanar cikin mahaifiyar, mijinta da ya dade baya gida yace ba nashi bane.

Da take bayyana yanda lamarin ya faru a ofishin 'yansandan kamar yanda Jaridar Vanguard ta ruwaito, mahaifiyar ta bayyana cewa wata rana cikin dare taji wani yaro me kama da danta ya shigo mata daki kuma abinda ya faru ya faru kuma ta kasa magana.

Shima dai yaron da ake kira da Ekenem ya bayyana cewa ya gwadane, baisha cewa lakanin da Bokan ya bashi zai yi aiki ba, inda yace da mahaifiyar tashi ta so fallasa maganar shine sai yayi barazanar kasheta amma yace yana fatan zata yafe masa.

Hukumar 'yansanda ta bayyana cewa, ta kama yaronne saboda barazanar rayuwar da yayi.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment