Thursday, 19 December 2019

Yanda na kama Sakon 'yan mata a wayar Mijina, Sani Danja>>Mansurah Isah

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, wadda a yanzu ta shahara wajan baiwa gajiyayyu tallafi,Matar Tauraron fina-finan Hausa, Sani Danja, Zaki watau Mansurah Isah a tattaunawar da ta yi da shirin Daga Bakin Mai Ita na BBChausa ta bayyana yanda take kama sakonnin 'yan mata a wayar mijinta.

Da aka mata tambayar cewa shin yaushe Sani Danja Zai matankishiya? Mansurah ta ce ba rana balle wata.

Ta yi karin haske kan cewa aurene yasa ta daina fitowa a Fim saboda idan mutum yayi aure akwai abubuwan da dole zai hakura dasu, saboda fim ba zama guri daya, shiyasa ta koma harkar kungiyarta ta tallafawa jama'a tace duk da itama akwai tafiye-tafiye amma dai ba'a fitowa a fim.

Mansurah ta amsa tambayar cewa an taba marinta? Da, saboda rashin jinta lokacin tana yarinya, akwai sanda yayanta ya taba zane ta. Tace saboda kiriniya har da 'yan daba ta yi fada.

Tace bayyana Samira Ahmad a matsayin babbar kawarta.

Da aka tambayeta ko ta taba kama sakon 'yan mata a wayar mijinta? Mansurah ta bayyana cewa da yawa ma,tace shi sanannen mutum ne kuma gashi fari kyakkyawa, kuma yana da 'yan canjinshi, to idan bai musi ba su zasu mai.

Tace wani lokacin takan kauda kai, wani lokacin kuma ta tambayeshi inda yake bata amsar cewa, cikin buhu-buhunnan ne daya zazzage wasu suka makale.

Da aka tamyeta sirrin zamam aure, Mansurah ta karfafa Hakuri sosai sannan tace da kauda kai.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment