Pages

Monday 9 December 2019

'Yar kasar Africa ta kudu ta lashe gasar Sarauniyar kyau ta Duniya

'Yar kasar Afrika Ta Kudu, Zozibini Tunzi me shekaru 26 ta lashe kambun Sarauniyar Kyau ta Duniya da na shekarar 2019 da aka yi a kasar Amurka jiya, Lahadi.



Tunzi itace bakar mace ta farko daga kasar Africa ta kudu da ta taba lashe wannan kyauta.


Ta bayyana cewa, taje wannan gasa da Gashinta na Asali da kuma kalar fatarta ta Asali saboda tana fafutukar karfafawa maa su tsaya da irin kyawun da Allah ya musu ba sai sunyi karn gashi ko canja kalàr fatar jikinsu ba.


Bayan lashe kyautar aka kuma dora mata kambun da aka yi na zinare a kai wanda aka kiyasta kudinshi sun kai Dalar Amurka Miliyan 5, kwatankwacin Sama da Naira Biliyan 1.8, Bunzi tace ta taso a inda ake kallon matan dake da fata irin tata da kuma gashi irin nata da cewa su ba kyawawa bane, dan haka tana son duk wata yarinya irinta ta kalle ta a matsayin abin karafafa gwiwa.





Ta kuma yi kira da baiwa mata jagorancin a bangarori daban-daban inda take kalubalantar kaskancin da ake nunawa mata musamman bangaren shugabanci.

'Yar kasar Puerto Rico ce ta zo ta 2 yayin da 'yar kasar Mexico ta zo ta 3.

'Yar Najeriya kuwa wadda hotonta ke kasa tazo ckin 20 na farko ne.

Mata 90 ne suka shiga gasar ta bana.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment