Tuesday, 3 December 2019

'Yar uwar Ronaldo ta caccaki Van Dijk bayan da yawa Ronaldon ba'a

'Yar uwar tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo watau Katia Aveiro ta caccaki dan wasan Liverpool, Virgil Van Dijk bisa ba'ar da yawa dan uwanta Ronaldo jiya a wajan bayar da kyautar Ballon d'Or.Kafar watsa labarai ta kasar Netherlands, RTL7 da take hira da Van Dijk a daren jiya wajan bayar da kyautar ta bayyana mai cewa tunda Ronaldo be halarci wajan bayar da kyautar ba daya daga cikin abokan takararshi ya ragu kenan, Sai Van Dijk ya bayar da amsar cewa to ai ya zama ba abokin takara ba kenan.

Wannan yasa Katia ta fito ta caccaki Van Dijk inda ta bayyana cewa dan uwanta Ronaldo ba sa'anshi bane a harkar kwallo dan ya ci kyautukan karramawa da yawa dan haka ya bari sai shima ya ci irinsu sannan ya fara kawo kanshi kusa da Ronaldo.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment