Sunday, 1 December 2019

Za Mu Amince Da Duk Wata Doka Da Za A Gindayawa Barayin Gwamnati, Amma Ban Da Hukuncin Kisa>>Majalisar Dattawa

Majalisar dattawa ta ce ba zai yiwu a kirkiro da dokar kisa ga mahandama ba. Amma kuma, majalisar dattawan ta ce a shirye take da ta goyi bayan wasu hukuncin da za a yi wa mahandaman. 


Mai magana da yawun majalisar, Godiya Akwashiki ne ya sanar da hakan yayin zantawarsa da 'yan jaridu. 

Ya yi magana ne a kan yadda wasu ‘yan Najeriya ke kira ga majalisar a kan ta yankewa masu wawurar kudin kasa hukuncin kisa, a maimakon masu kalaman kiyayya a kafafen sada zumuntar zamani. 

Akwashiki ya kara da yin bayanin cewa, ba zai yiwu shugaban majalisar dattawan ya umarci wani sanata da ya miko wata bukata gaban majalisar ba, harda wanda ya hada da kisa ga mahandama.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment