Pages

Thursday 23 January 2020

A karin farko tun bayan sakinshi: Dasuki ya bayyana gaban Kotu

A karin farko tun bayan da gwamnatin tarayya ta sakeshi bayan tsaron shekaru 4 da ya sha duk da bayar da belinshi da kotu ta yi a lokuta daban-daban, Tsohon me baiwa shugaban kasa shawara akan tsaro Sambo Dasuki ya bayyana a gaban babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja.



A sauraren karar da alkali Ahmed Muhammad yayi Sambo Dasuki ya janye tirjiyar daya nuna na kin zuwa Zaman kotun saboda kin bada belinshi da aka yi inda ya bayyana cewa hakan na farune dalilin sakinshi da gwamnatin tarayya ta yi.

Ofishin me baiwa ahugaban kasa shawara kan shari'a na zargin Sambo Dasuki da Almundahanar kudi da kuma mallakar makamao ba bisa ka'aida ba, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Saidai a zaman shari'ar na yau Punch ta lura cewa, akwai wasu tuhume-tuhume da akewa Dasuki a baya da a yau din ba'a karantosuba.

Punch tace ta lura akwai alamar nutsuwa tattare da Dasukin a wannan zaman fiye da sauran zaman kotun da yake zuwa a lokacin yana tsare a hannun gwamnati.

Kotun ta daga sauraren karar zuwa 11 da 12 ga watan Maris.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment