Wednesday, 15 January 2020

An kai wa Sarkin Potiskum hari a Kaduna

Wasu mahara sun kai wa Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, hari inda suka kashe mutum shida, kamar yadda rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta bayyana.


Kakakin Rundunar 'Yan sanda a jihar Kaduna DSP Yakubu Abubakar Sabo ya tabbatar wa da BBC faruwar al'amarin.

DSP Sabo ya ce abin ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, a kusa da garin Marabar Jos da misalin karfe 11:00 na daren ranar Talata.

Ya ce wasu mahara ne suka bude wa ayarin motocin sarkin wuta wanda hakan ya yi ajalin mutum shida - biyu fasinjoji da ke tafiya a hanyar, hudu kuma daga cikin jama'ar sarkin.

Hakazalika ya ce tun farko 'yan bindigar ba sarkin suka hara ba.

Ya ce sun tare wata babbar mota ce dauke da fasinjoji da ke kan hanyarta ta zuwa Kaduna.

Ana cikin haka ne sai ga tawagar sarkin tare da jiniyar masu yi masa rakiya, abin da ya sa 'yan bindigar suka yi zaton jami'an tsaro ne kuma hakan ya sa suka fara bude wuta, in ji kakakin 'yan sandan.

Har ila yau mun tuntubi diyar sarkin Fatsima Umar kuma ta shaida mana cewa dogaran sarkin uku ne suka mutu da kuma wani direbansa daya.

Kuma ta ce sarkin yana cikin koshin lafiya tun bayan faruwar al'amarin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment