Wednesday, 15 January 2020

An kwace wa mutanen Imo gwamnan da suka zaba>>PDP

Babbar Jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP ta ce ta yi mamakin hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Imo


A ranar Talata ne kotun koli ta kwace kujerar gwamna daga Emeka Ihedioha na Jam'iyyar PDP ta ba Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sanarwar da kakakin jam'iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar bayan zartar da hukuncin ta ce, PDP ta kasa fahimtar dalilan da kotun koli ta yi dogaro da su na yanke hukuncin.PDP ta kasa fahimtar yadda za a ce dan takarar da ya zo na hudu a zaben gwamna na 9 ga Maris da kuri'a 96,458 ace ya doke dan takarar PDP da ya samu yawan kuri'u 276,404

A nata bangaren, jam'iyyar APC ta bayyana farin cikinta da hukuncin Kotun kolin da ta bayyana dan takararta Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Imo.

APC ta ce duk da cewa ta yi mamakin yadda ta rasa kujerar gwamna a jihar Zamfara a kotun koli da kuma yadda kotun ta haramta ma ta shiga zabe a Rivers amma hakan bai sa ta cire tsammani ba kotun.


PDP ta ce an sauya wa mutanen Imo wanda suka zaba aka ba wanda mutanen jihar ba su ra'ayin shi a zaben da aka gudanar.

Ta ce yanzu duk nasarori da ci gabada kuma kwanciyar hankali da aka samu karkashin gwamna Emaka Ihedioha ya tafi a banza.

Jam'iyyar PDP kuma ta yi kira ga magoya bayanta a jihar Imo su kai zuciya nesa tare da rungumar kaddara kan hukuncin kotun.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment