Thursday, 16 January 2020

An Samu Matar Dan Majalisar Da Aka Sace A Jihar Jigawa

Bayan shafe kwanaki Biyar da sace matar dan majalisar dokoki na jihar Jigawa, wanda ke wakiltar karamar Hukumar Miga, Hajiya Zara'u da wasu masu garkuwa da mutane suka yi, a jiya Laraba Allah ya bayyana ta.


An samu Hajiya Zara'u dai cikin koshin lafiya, bayan ta dawo gida da misalin karfe 11:00 na daren jiyan.

Idan ba a manta ba dai, tun ranar Juma'ar da ta gabata ne wasu masu garkuwa da mutane suka shiga har gidanta dake garin Dangyatin dake karamar Hukumar Miga  suka yi awon gaba da ita

Kawo yanzu dai rundunar 'yan sanda ta jihar Jigawa ba ta fadi irin hanyoyin da suka bi wajen samo wannan mata ba, domin wakilinmu na jihar Jigawa ya kira lambar makogoron 'yan sanda na jihar, SP Abdul Jinjiri bai cira ba, har lokacin hada wannan rahoton.

Yanzu haka Haj. Zara'u na cikin iyalanta a garin na Dangyatin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment