Pages

Sunday 26 January 2020

Ana iya kamuwa da cutar Zazzabin Lasa ta hanyar ta hanyar jima'ai>>Masana

Wata Likitar dake kula da bangaren ciwon Zazzabin Lasa a Asibitin Koyarwa na jami'ar gwamnatin tarayya dake Jihar Ebonyi,Nnenna Ajayi ta yi gargadin cewa ana iya samun cutar ta Lassa a wajan jima'ai.



Da farko dai ta bayyana cewa ana samun cutarne daga dabba, watau Bera wanda idan ya taba abinci ko kuma wasu kayan da dan Adam ke amfani dashi to za'a iya kamuwa da cutar, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Ta kara da cewa idan cutar ta shiga jikin dan Adam yakan iya gogawa sauran mutane ta hanyar Jini ko sauran ruwayen dake fita daga jikin Mutum sannan ana daukar Cutar ta hanyar Jima'ai ko uwa me dauke da juna Biyu ta gogawa Jaririnta.

Alamomin cutar kamar yanda likitar ta bayyana sune, akwai zazzabi, Rashin jin dadin baki Amai da gidawa, Idon mutum yakan yi jaa, sannan jikin mutumn yakan tika fitar da jini.

Da take bada shawarar yanda za'a iyaye kamuwa da wannan cuta tace a rika rufe kofofi da kyau sannan a tabbatar babu wani huji a jikin katanga ta yanda Bera ba zai iya shiga ba, hakanan Masu farautar Bera su ci suma su hakura da wannan abu, tace idan an Jiye abinci a tabbatar an kulle da kyau ta yanda koda Bera ya je ba zai iya budeshi ba.

Ta bada shawarar cewa idan so samune ace mutum ya takaita cin abincin saye, ya rika dafa abincin da zai ci da kanshi, idan kuma ta kama sai ya saya a waje to ya sayaninda yake ganin akwai tsafta.

Ta kuma yi gargadin barin shara ba tare da zubar da ta ba saboda beraye kan je shara dan nan sauran abinci da kuma dena yadda abinci a kusa da gida dan kada hakan ya jawo berayen.

Allah ya tsaremu.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment