Pages

Sunday 26 January 2020

Babban Bankin Nijeriya, CBN Ya Fara Tsorata Da Yawan Bashin Da Najeriya Ke Ciwowa Daga Kasashen Waje

Babban Bankin Nijeriya, CBN ya gargadi Najeriya cewa yawan bashin da ake ciwowa da sunan ayyukan inganta tattalin arziki, ya na neman zama luma wa ciki wuka, matsawar gwamnatin tarayya ba ta yi gaggawar yin taka-tsantsan ba.


Wannan jan-kunne ya fito ne daga bakin Kwamitin CBN Mai Sa-ido Kan Tsare-tsaren Kashe Kudade, MPC.

Kwamitin ya ce dalilin da gwamnati ke bayarwa cewa ta na kara lafto bashi ne domin inganta arzikin kasar nan, ba abin dogaro ba ne, idan aka yi la’akari da cewa yawan bashin da ake ciwowa ya haura yawan kudaden shigar da gwamnati ke samu a nan cikin gida da kuma masu shigowa daga kasashen waje.

MPC ta yi wannan bayani ne a Abuja, bayan tashi daga taron ta na 271, wanda kwamitin ya shafe kwanaki biyu ya na gudanarwa.

Shugaban Bankin CBN, Godwin Emefiele ne da kan sa ya sa wa takardar bayan taron hannu, kuma aka taba wa ‘yan jarida a ranar Juma’a, bayan tashi daga taron.

“Ba dabara ba ce a rika ciwo bashi, har kudin bashi ya na yin yawa fiye da kudaden shigar da kasar nan ke samu a nan cikin gida da kuma kudaden shigar da ke zuwa daga waje.”

Shawarar MPC Ga Gwamnati
Daga nan sai MPC ta bada shawarwari kamar haka:

A rika rage kudaden da Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi ke rabawa a duk karshen wata a tsakanin su. 

Wannan hikimar za ta sa wadannan kudaden da ake ragewa, za su hana Najeriya afkawa cikin kuncin tattalin arziki a duk lokacin da farashin danyen mai ya karye a kasuwar duniya.

Shawara ta biyu da Kwamitin MPC ya bai wa Gwamnatin Tarayya ita ce, a rage dogaro da ribar kudaden cinikin danyen mai. 

A fadada hanyoyin samun kudaden shiga a cikin kasa, wadanda za su rika ko kara samar wa gwamnati kudaden haraji.

Shawara ta uku kuma ita ce, gwamnati ta rage kashe kudade wajen ayyukan tafiyar da sha’anin mulki da gwamnati a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyi.

Wannan gargadi da CBN ya yi wa gwamnati ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke kokarin ciwo bashin dala biliyan daya, wato kwatankwacin naira bilyan 360, domin ta sayo kayan noman da za ta raba wa manoma a fadin kasar nan.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment