Tuesday, 14 January 2020

Barcelona ta kori kocinta, Ernesto valverde

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kori kocinta, Ernesto Valverde daga aiki inda ta maye gurbinshi da tsohon kocin Real Betis, Quique Setein wanda shima Real Betis korarshi ta yi duk da ya mata kokari.Barcelona na saman teburin Laliga inda kuma ta kai matakin gaba na gasar Champions League inda zata hadu da Napoli.

Saidai Atletico Madrid ta fitar da ita daga gasar Super Cup da ci 3-2 a wasan kusa dana karshe na gasar.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment