Tuesday, 14 January 2020

Direban A Daidaita Sahu (Keke Napep) Ya Ɗauki Nauyin Karatun Wasu Yara Marayu A Jalingo

A jiya Litinin, wani matukin Keke Napep dake birnin Jalingo, mai suna Abubakar Umar, ya sanya wasu yara marayu da waɗanda iyayensu basu da karfi har su 30 makarantar firamari, inda ya yi alkawarin cigaba da ɗaukar ɗawainiyyarsu har zuwa aji shida.


Hakika wannan bawan Allah ya yi abinda wasu zaɓabɓun 'yan siyasa suka gagara yi wa al'ummar da suka zaɓe su.

Muna addu'ar Allah ya ɓuɗa masa ya ba shi ikon cika wannan alkawari da ɗauka.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment