Sunday, 12 January 2020

Duk da Jan Katin daya Samu Valverde ya sha yabo sosai a wasan da Real Madrid ta dauki Super Cup

Bayan da lokacin tashi wasa yayi babu wanda ya saka kwallo taskanin kungiyoyin Real Madrid da Atletico Madrid a wasan da suka buga yau na gasar cin kofin Super Cup, dole aka kara lokaci, a mintuna 116 na wasan, Alvaro Morata ya dauki kwallo inda yayi tsirara daga shi sai gola amma dan wasan Real Madrid Valverde ya tadiyeshi.Dalilin haka, alkalin wasa bai yi wata-wata ba ya baiwa Valverde jan kati. Saidai duk da haka Valverde ya sha yabo wajan magoya bayan Real Madrid da dama dan kuwa da ace Morata ya ciwa Atletico Madrid din kwallonnan to da shikenan kashi Real Madrid ya kare a wasan.Shima dai Kocin Atletico Madrid sai da ya jinjinawa valverde inda yace koma wanene avinda zai yi kenan.

Da ake hira dashi bayan kammala wasan, Valverde ya bayyana cewa abinda ba makawa sai yayine yayi amma ya baiwa Morata hakuri.

Valverde da golan Real Madrid Curtoise sun sha yabo sosai a wasan na yau saboda bajintar da suka nuna.

Kalli bidiyon lamarin a kasa:

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment