Saturday, 25 January 2020

GARGADI GA MASU SAYEN NAMA BALANGU KO TSIRE

Mun sani cewar ana nade su (tsire ko balangu) idan mun saya a cikin takardun makarantu ko jaridu.


Yana da kyau mu sani cewar akasarin wadannan takardun ana samo su ne daga dakin ajiye kaya (store) na makarantu. 

Wanda a cikin dakin ajiye kayan akwai bera, jaba, kyankyaso, tsaka da sauransu. Suna yin kashi da fitsari a kai, amma haka za a dauko su a kunsa mana gasasshen nama a ciki muna ci. 

Hakika wannan babban kuskure ne kuma yana iya haddasa mana cututtuka.

Don Allah a kula!

Allah ya kara tsare mu.

CopiedKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment