Thursday, 16 January 2020

Gasar dake tsakanina da Ronaldo Zata ci gaba har Abada>>Messi

Tauraron dan kwallon kasar Argentina me bugawa kungiyar Juventus wasa, Lionel Messi ya bayyana cewa, gasar dake tsakaninshi da Ronaldo zata ci gaba da zama har abada.DAZN ta ruwaito Messi yana cewa, gasar da suke da Ronaldo abune da ya dauki shekaru suna yi kuma zata ci gaba har illa masha Allah.

Ya kara da cewa gasar dake tsakaninsu abune me daukar hankali da kayatarwa musamman tsakanin masoya kwa─║lon kafa.

Messi ya ciwa Barcelona jimullar kwallaye 472 yayinda Ronaldo ya ciwa Real Madrid jimullar 450, kamin ya koma Juventus da wasa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment