Tuesday, 14 January 2020

Gidan Tauraron fina-finan Hausa, Aminu Acid yayi Gobara

A JIYA Lahadi, 12 ga Janairu, 2020 gobara ta tashi a gidan fitaccen jarumi Aminu Ilu Dambazau da ke Kano, ta ƙone dukkan gidan da abin da ke cikin sa ƙurmus.

Wutar ta faru ne wajen misalin ƙarfe 11 na rana a gidan jarumin da ke unguwar Shagari Quarters.

Tsohon jarumin, wanda aka fi sani da Aminu Asid, ya labarta wa mujallar Fim yadda abin ya faru, ya ce, "Ni dai abin da na sani shi ne na fito da safe, kuma iyali na sun fita unguwa, da man akwai wani maƙocin mu da zai tare a gidan sa, to ta je ta raka su, kawai misalin 11 na rana sai wani maƙoci na ya kira ni a waya ya ke sanar da ni gida na ya kama da wuta na yi sauri na je."

Aminu ya ƙara da cewa, "Ina zuwa kusa da gidan, sai kawai na ga baƙin hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya, kuma babu wata dama ta shiga gidan domin gaba ɗaya gidan ya kama da wuta ne.

"Duk da haka, na yi ta ƙoƙarin shiga gidan, amma sai maƙota na su ka riƙe ni, domin tunani na duk wasu kaya na da su ke da muhimmanci duk za su ƙone, amma haka dai aka riƙe ni na tsaya ina kallon ƙudirar Ubangiji.

"Wutar ta rinƙa ci, babu abin da na iya yi sai kiran sunan Ubangiji, kuma duk da jami'an kashe gobara mota shida sun zo wajen, amma wutar sai da ta kai har wajen ƙarfe 3 ta na ci ba tare da ta mutu ba."

Dangane da irin asarar da aka yi kuwa a gidan, Aminu ya ce, "To gaskiya, asarar da zan ce ba a yi ba sai ta rai, amma duk wani abu da na mallaka a gidan da ni da iyalai na, babu abin da ya yi saura, domin kayan da mu ka fita da shi na sakawa a jikin mu to shi kaɗai ya yi saura, amma duk abin da mu ka mallaka da ni da iyali na duk sun ƙone, kamar abin da ya shafi takardun makaranta, kayan buƙatu na gida da duk wani abu da ka sani duk sun ƙone.

"Don haka a yanzu ni da mu ke hirar nan da kai ni kaɗai na san abin da na ke ji, don ba don addu'ar da na ke yi ba, ban san yadda zan samu kai na ba."

Tuni dai 'yan'uwa 
da abokan arziki su ke ta yin tururuwa zuwa gidan domin jajanta masa kan abin da ya faru.

Cikin masu jajanta wa jarumin har da ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya, wato 'Motion Picture Practitioners Association of Nigeria' (MOPPAN).

A cikin wata sanarwa, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na ƙungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, ya ce, "A madadin shugaban MOPPAN na ƙasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, da dukkanin shugabanni a matakin ƙasa da na jihohi, da ilahirin membobin MOPPAN baki ɗaya, ina miƙa saƙon jaje zuwa ga ɗan'uwan mu Malam Aminu Acid, bisa wannan ibtila'in da ya same shi a daren jiya.

"Mu na masa fatan hakan ta kasance jarrabawa ce a gare shi, Allah Ta'ala ya mayar masa da dubun alherin da ya salwanta sakamakon wannan gobarar.

"Haka kuma mu na miƙa wannan jajen ga maiɗakin sa, 'yan'uwan sa, iyaye da abokan arziki.

"Allah ya kiyaye na gaba, amin."Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment