Wednesday, 15 January 2020

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Baiwa 'Yan Bindiga Awanni 24 Da Su Sako Duk Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Su Ko Kuma Su Dandana Kudarsu

A kokarin gwamnatin na kawo karshe kashe-kashe da sacen-sacen mutane da ya addabi wadansu kananan Hukumomi jihar Katsina, gwamnatin jihar ta yi wa 'yan bindigar gargadi na karshe na ko dai su rungumi sulhun da gwamnatin jihar ta kulla da su ko Kuma ta dauki kwakkwaran mataki na ganin hukumomin tsaro sun kakkabe su.


Shugaban kwamitin sasancin tsakanin Gwamnatin jihar Katsina da kuma fulanin kuma Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana haka, bayan kammala zaman da yan bindigar da suka rungumi sulhu da Hukumomi tsaro da ke aiki a jihar Katsina, domin tabbatar da tsaro wanda ya gudana da marecen yau a tsohon gidan Gwamnatin jihar Katsina.

Mustapha Inuwa ya yaba da irin gagarumar guddummuwar da 'yan bindigar da suka rungumi sulhu ke baiwa jami'an tsaro da kuma gwamnatin jihar Katsina, musamman a yankin kudancin Katsina, ta hanyar da suke bada bayanan sirrin ga jamian tsaro, wanda kuma yana haifar mana da da mai ido. Kuma mun nemi su cigaba da bada wannan hadin kai, kuma gwamnatin za ta cigaba da taimaka masu.

Shugaban kwamitin Kuma Sakataren Gwamnatin jihar Katsina, ya kara da cewa su kuwa wadanda suka ki bada wannan hadin kai, na wajen kananan hukumomin Jibia da Batsari da masu shigowa Kurfi da Dutsinma da wani bangare na Matazu da kuma Musawa. Mun gaya masu cewa wannan shi ne taron sulhu na karshe da za a zauna a tattauna tsakanin mu da su akan maganar sasancin, ko dai su karbi zaman lafiya ta hanyar sulhu, ko kuma a aiwatar da abinda ake guje masu jami'an tsaro su zo su shiga su ida kakkabe su.

Mustapha Inuwa ya cigaba da cewa wadanan mutane da suka kama suke garkuwa da su a dajuka daban daban, musamman na Jibia da Batsari, da su gaggauta sako su ba tare da wani sharadi ba, nan da zuwa ranar alhamis, ko kuma duk abinda ya faru su suka jawa kansu, saboda wannan al'amarin ya kai karshe wato karshen tika-tika tik. Saboda haka mai son zaman lafiya ya rungume shi, wanda kuma baya so zai dandana kudarsa.

Inuwa ya ce za mu yi amfani da karfin soja da kuma sauran jamian tsaro da ke aiki a jihar Katsina domin ganin mun samu zaman lafiya mai dorewa a jihar Katsina da kuma arewa maso yammacin Nijeriya wato Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi. Kusan daga wannan Wa'adin da muka basu babu maganar sassauci tsakanin mu da wadannan yan bindigar ba. Saboda wadanan kalilan din daga cikin su ba za mu bari su lalata mana zaman lafiya ba, maganar a zauna lafiya ko kuma jamian tsaro su cigaba da yi masu luguden wuta ne a mafakarsu.

Taron ganawar ya samu halartar wasu daga cikin fulanin daji wadanda suka rungumi sulhun da gwamnatin jihar Katsina ta yi da su a watannin baya da Shugaban rundunar sojoji da ke Sokoto Janar Aminu Bande da Shugaban Yansanda ciki da Kwamishinan Yansanda na jihar da Kuma na farin kaya wato civil defense.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment