Tuesday, 14 January 2020

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Haramta Yin Wa'azi A Fadin Makarantun Jihar

Gwamnatin jihar Kwara ta haramtawa kungiyoyin addini yin wa’azi a makarantun gwamnati a duk fadin jihar.


Sanarwar wacce kwamishinan ilimi na jihar da ci gaban dan Adam, Hajiya Fatimoh Ahmed, ta bayar ta ce addu'o'i ya kamata adinga yi yayin babban taron safe.

A cewar kwamishinan, ba wata kungiya ta addini da aka yarda ta shiga makarantu don yin kowane irin nau'in ayyukan addini yayin taron safiya.

Ta kuma nemi shugabannin makarantu da su bi umarnin sosai, in ji ta, “ta samu sanarwar gwamnatin jihar Kwara cewa wasu kungiyoyin addinai suna zuwa makarantun gwamnati a jihar don yin wa’azi yayin taron asuba.

“Ma’aikatar tana son ta fadi hakan da cewa babu wata kungiyar addini da za ta ba ta izinin zuwa makarantun gwamnati don wa’azi ko kuma yin kowane irin addini a lokacin safiya.

“Saboda haka ma’aikatar ta ba da umarnin cewa a yi addu’o’i a hankali a taron safe a duk fadin makarantun gwamnati a jihar.

“Gwamnati tayi kira ga dukkan shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su bi wannan umarni, wanda shine kiyaye zaman lafiya da tsari a makarantunmu.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment