Pages

Friday 24 January 2020

Gwamnatin Tarayyar Ta Halatta Kungiyar Tsaron Amotekun

Mataimakin shugaban kasar ya gana da gwamnonin yankin kudu maso yannacin Najeriyar ne tare da Antoni Janar Abubakar Malami da kuma sufeton ‘yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar.


Mai Magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu Akande, yace gwamnonin ne suka nemi ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan batu dake cigaba da janyo mahawar. Ganin shugaban kasa na rangadi a Ingila ne ya nemi mataimakinsa ya jagoranci tattaunawar.

“Zama dai ya yi ma’ana kana an samu fahimtar juna a kan mataki na gaba game da batun” inji Akande a cikin wata sanarwar da ya fitar. Yace ganin yanda ake buakatar taimakon kowa a harkar tsaro da ta tabarbare a fadin kasar, wajibi ne a amince da rundunar Amotekun ta bada tsaro a unguwanni a kan tsarin gwamnatin tarayya.

Wani masanin tsaro Aliko El Rashid Harun ya bayyana fargabrsa ga wannn mataki da gwamnatin trayya ta amince da shi. Yace gwamnati ta yi amai ta lashe abinta ya kuma ce mai yiwuwa ne nan da ‘yan watanni kadan a samu rikici tsakanin jami’an tsaron tarayya da na jihohin da aka kafa karkashin rundunar Amotekun.

Su ko masana dokokin kasa kamar su Barista Yakubu Sale Bawa, suna gani kafa wannan rundunar tsaron bai sabawa dokokin kasa ba. Yace akwai tanadi da kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi na kafa kungiyoyin tsaro da zasu taimaka wurin samar da tsaro a cikin yankunan karkara, dan haka bisa ga wannan doka bai yiwuwa a haramta Amotekun.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment