Pages

Sunday 26 January 2020

Harin Kunar bakin wake da aka kaiwa Masallaci a Borno ya hallaka mutane 4

Harin kunar Bakin Wake ya hallaka mutane 4 a garin Gwoza dake kudancin jihar Borno. Lamarin ya farune a lokacin sallar Asuba inda aka samu wani dan kunar bakin wake ya afkawa wasu masallata.



Wata majiya ta bayyana cewa maharin da ba'a tantance namijine ke mace ba ya mutu tarre da wasu masallata 3. Saidai wata Majiyar tace Mutane 3 ne suka rasu a harin hadda maharin.

Majiyar tsaro da bata so a wallafata ta bayyana cewa maharinne kadai ya mutu sai kuma mutane 13 da suka samu raunuka.

Hukumar soji ko 'yansanda bata tabbatar da harin a hukumance ba.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment