Pages

Sunday 26 January 2020

Karancin Masu Shiga Jami’o’i Babbar Matsalace A Nijeriya, Cewar Shugaban NUC

Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Farfesa Abubakar Rasheed ya bayyana cewa akwai gagarimar matsalar da ke neman tunkarar kasar nan, ganin cewa dalibai ba su fi milyan biyu ba ne kacal jami’o’in kasar nan ke iya dauka.


Rasheed ya yi wannan jawabi mai cike da nuna damuwa ne, a lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Zagayowar Ranar Ilmi ta Duniya, a Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya, a New York, Amurka.

Ya ce bayan NUC ta yi la’akari da cewa akwai al’umma milyan 200 a Najeriya, to kuma bincike ya tantance cewa mutum milyan 2 ne kacal a jami’an.

“Matsalar sashin samun damar shiga jami’a da kuma rashin samun ingattacen ilmi, babban abin damuwa ne a kasar nan. Domin daga cikin al’umma mai jama’a milyan 200, kashi daya bisa 100 ne kadai ke jama’a. Wannan matsala ce, ba karama ba, gagarima ce sosai.” Inji Rasheed.

A Najeriya mu na da jami’o’i 172. Guda 79 daga cikin su mallakar coci-coci ne sai wasu kungiyoyin addinin musulunci. Sauran na Gwamnatin Tarayya da jihohi ne.’

Da Rasheed ya juya kan malamai masu koyarwa a jami’o’i, ya ce akwai su 61,000, wadanda cikin su kashi 17 bisa 100 ne kadai mata.

Batun bambancin jinsin yawan dalibai a jami’o’i kuwa, Rasheed ya ce dalibai mata sun fi dalibai maza yawa a jami’o’in da ba na gwamnati ba.

Yayin da a jami’o’i mallakar gwamnati kuwa, kashi 42 bisa 100 ne mata, kashi 58 bisa 100 kuma maza.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment