Thursday, 16 January 2020

Kashmir: An gano yarinya da ranta bayan shafe sa'a 18 a karkashin kankara

An gano wata yarinya mai shekara 12 a raye bayan da dusar kankara ta rufe ta tsawon sa'o'i 18 lokacin da tudun kankara ya zabtaro kan gidanta a yankin Kashmir.


Samina Bibi ta ce "ta yi ta kurma ihu tare da neman taimako" lokacin da abin ya rutsa da ita kamar yadda ta shaida wa Reuters.

Ta ce kafin a kai mata dauki, ta dauka ta mutu ne.A 'yan kwanakin nan, Kwarin Neelum ya fuskanci matsalar zabtarowar dusar kankara da murginowar laka wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutum a kalla 74.

Yayin da yankin Himalaya yake yawan fuskantar rashin kyawun yanayi, adadin mutanen da suka mutu sun fi yawa a tarihi.

Al'amarin ya shafi yankin Kashmir da ke karkashin Indiya da Afghanistan, amma bangaren Kashmir da ke karkashin Pakistan da kuma Kwarin Neelum sune al'amarin ya fi shafarsu.

Masu kai agaji suna ci gaba da kokarin lalubo mutanen da suka yi batan dabo.

'Al'amarin ya faru cikin kiftawar ido'

An ceto Samina daga kauyen Bakwali inda aka kai ta asibiti a Muzaffarab. Amma da yawa daga cikin 'yan uwanta sun mutu.

Mahaifiyarta, Shahnaz Bibi, ta ce iyalinta sun yi da'ira a gaban wuta suna jin dimi a gidansu mai hawa uku lokacin da dusar kankarar ta fara zaftarowa.

"Bamu ji wata alama ba. Abin ya faru cikin kankanin lokaci," a lokacin da take fada wa Reuters cewa ta yanke kaunar za a gano 'yar tata da rai.

Samina ta bayyana cewa ta samu karaya a kafarta kuma jini yana ta fita daga bakinta.

A cewarta, ba ta iya bacci ba yayin da take jiran a kai mata dauki.


A sassan Pakistan, a kalla mutum 100 ne suka mutu a yankunan da suka fuskanci matsalar zabtarowar dusar kankara, a cewar hukumar kula da bala'o'i ta kasar.

Mutum takwas sun mutu a Jammu da Kashmir da ke karkashin Indiya, a cewar kafafen yada labaran kasar.

Kashmir na da murabba'in kilomita 86,000 kuma a zagaye yake da kyawawan tafkuna da ciyayi.

Sai dai yankin na fama da rikici na tsawon shekaru kuma yanzu yana karkashin Indiya da Pakistan tun bayan da kasashen biyu suka samu 'yancin cin gashin kansu a 1947.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment