Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa duk da kokarin gwamnati na ganin ta tallafawa al'ummar kasarnan, har yanzu mafi yawancin 'yan Najeriya basu amfana da tsarin na tallafin jama'a ba.
Yace irin wannan kokari na kamfanonine zai cike gibin da gwamnati ta bari wajan tallafin da take baiwa Al-umma.
Ya bayyana cewa gwamnatinsu tana ciyar da yara Miliyan 9.5 a makarantu a jihohi 34 na kasarnan sannan kuma akwai tallagin kudi da ake baiwa wasu mutane kusa Miliyan a fadin kasarnan.
Ya kara da cewa akwai kuma matasa Dubu 500 da aka dauka aikin N-Power. Saidai yace duk da haka akwai 'yan Najeriya da dama da basu amfana da wannan tsare-tsaren na gwamnatin ba dan haka suke bukatar karin himma wanda kuma sai sun zuba kudade masu yawa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole
No comments:
Post a Comment