Wednesday, 15 January 2020

Masari Ya Sanya Hannu Kan Dokar Hana Hawan Babur Da Kurkura Da Dare

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya sanyawa wata dokar hana hawan babur tun daga karfe bakwai na dare zuwa karfe shidda na safe, saboda magance matsalar masu garkuwa da mutane. Dokar wadda ta shafi kowacce Karamar Hukumar jihar talatin da hudu.


Kwamishinan Sharia na jihar Katsina, Alhaji Ahmad El'marzuq ya bayyana haka, jim kadan bayan Gwamna Aminu Bello Masari ya sanyawa dokar hannu a gidan Gwamnatin jihar Katsina.

El'marzuq ya kara da cewa dokar za ta fara aiki a ranar litinin 20/01/2020. Amma ba ta shafi Maaikatan tsaro ba, suna da damar hawan baburansu a kowane lokaci. Kuma duk wanda aka kama ya karya dokar zaa daure shi shekara guda a gidan yari kamar yadda dokar ta tanada, wadda gwamnan ya sanyawa hannu a yau.

Kwamishinan ya cigaba da cewa gwamnati ta dauki wannan matakin sakamakon mafi yawancin ayyukan taaddanci da satar mutane ana aiwatar da shi ne akan babura da 'yar kurkura a wadanan kananan hukumomin har da fadin jihar.

Daga karshe Kwamishinan El'marzuq ya yi kira ga alummar jihar Katsina da su bada hadin kai ga wannan dokar, da baiwa jamian tsaro hadin kai, domin samun ingantaccen tsaro a duk fadin jihar Katsina.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment