Pages

Sunday 26 January 2020

Mata ta kai mijinta kara a kotu a Sokoto saboda bai iya gamsar da ita a Gado

Wata mata mai sun Adama a jihar Sakkwato ta maka mijinta a kotun Majistre dake karamar hukumar Bodinga a jihar inda ta nemi hakkinta na kwanciyar aure da mijinta baya biya mata.



Matar ta gayawa kotu cewa mijin nata yana kokari wajan Kawo Abinci da mata Sitira, saidai wajan kwanciyar aurene ya kasa gamsar da ita.

Ta kara da cewa watanni 5 kenan be nemeta ba kuma ta yi iya yinta wajan jawo hankalinshi kanta amma a banza.

Saidai a nashi martanin mijin ya karyata matar tashi inda yace Rikici ne suka yi tsakaninsu saboda tana kokarin kawo mishi wani Kato cikin gida shiyasa ta kawo kara. Yace tabbas ya dauki lokaci me tsawo be nemeta ba amma baikai lokacin data gayawa Kotu ba.

Kotu ta tambayi mijin shin ko yana da matsalar mazantaka amma yace ko kadan kawai fadan da suka yi ne yasa ya kauracewa matarshi amma garau yake. Alkalin kotun ya dake sauraren shari'ar zuwa 4 ga watan Fabrairu, kamar yanda PM Express ta bayyana




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment