Tuesday, 14 January 2020

Matashin da ake zargi da kirkirar labarin auren karya na shugaba Buhari na fuskantar hukuncin shekaru 3 a gidan yari

Kabir Muhammad, Matashinnan da ake zargi da kirkiro bidiyon auren karya na shagaban kasa, Muhammadu Buhari da ministar Ibtila'i, Sa'adiya Unar Faruq na fuskantar hukuncin shekaru 3 a gidan yari idan aka sameshi da laifi.A ranar Talata, 14 ga watan Janairu ne hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS ta gurfanar da Kabir a gaban kotun Magistre dake Kano inda ake zarginshi da karya da kuma bata suna.

Idan dai aka samu Kabir da laifi to zai yi zaman gidan yari na shekaru 3 ba tare da zabin biyan tara ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment