Sunday, 12 January 2020

Matashiya ta kashe kanta sanadin rashin Likes a hotunanta

Wata baturiya, Chloe Davison me shekaru 19 ta kashe kanta sanadiyyar rashin likes da yawa a hotunanta da take sakawa a shafukanta na sada zumunta.Chloe ta kasance me son amfani da Shafukan sada zumunta sosai inda har ya zamana ta ware kanta a daki bata shiga cikin mutane sosai. Kuma takan yi iya bakin kokarinta dan ganin ta dauki hotuna masu kayatarwa da zata saka a shafinta na sada zumunta.

Mahaifiyarta ta bayyanawa Thesun UK cewa, tana samun sakonni daga wasu mazan na batsa da kuma na cin zarafi wanda a wasu lokutan take komawa gefe taita kuka.

Tace dalilin mutuwar diyar irin zagi da cin zarafin da ake matane a shafukan sada zumunta ya kashe diyarta.

Idan Chloe ta saka hotuna a shafinta na sada zumunta kuma hotunan basu samu likes da yawa ba to takan ciresu ta kuma shiga damuwa sosai irin hakane har yasa ta kashe kanta.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment